IQNA

Imam Khomeini (RA) Ya Raya Tunanin Kalubalantar Yahudawan sahyuniya

13:26 - June 06, 2011
Lambar Labari: 2133656
Bangaren kas ada kasa, marigayi Imam Khomeini (RA) ya raya tunain kalubalantar yahudawan sahyuniya 'yan mamaya, tare da zaburar da al'ummar musulmi da dukkanin 'yantattu na duniya wajen shiga kafar wando daya da su, da kuma kwato yankunan da suka mamaye a cikin palastinu da kuma kasar Lebanon.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wani daya daga cikin masana da ya halartci taron tunawa da marigayi Imam Khomeini da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeini (RA) ya raya tunain kalubalantar yahudawan sahyuniya 'yan mamaya, tare da zaburar da al'ummar musulmi da dukkanin 'yantattu na duniya wajen shiga kafar wando daya da su, da kuma kwato yankunan da suka mamaye a cikin palastinu da kuma kasar Lebanon da ma wasu kasashen yankin.

A wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo an bayyan acewa, daya daga cikin fitattun malaman addini kuma masana daga kasar Burma Ali Muhammad ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeni ya yi amfani da salo na ilimi wajen shiryar da mutane zuwa ga sahihin tafarkin koyarwar addinin muslunci wanda hakan kuma shi ne mabudin dukkanin nasarar da ya samu.
Malamin wanda daya ne daga cikin fitattaun malaman addinin Musulunci kuma masana a kasar Bama, ya bayyana cewa Imam Khomeini (RA) ya bayar da gudunmawa ga al'ummar muslumi, wadda har duniya ta nade ba za a taba mantawa da shi ba, domin kuwa ya kafa tafarki na yin aiki da koyarwar addinin muslunci tare da fadakar da al'ummar musulmi nauyin da ya rataya kansu.


803241


captcha