IQNA

15:20 - June 13, 2011
Lambar Labari: 2137571

Taron Bahasi Kan Kyamar Musulunci A Cikin Al’ummomin Nahiyar Turai

Bangaren kasa da kasa, ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bayyana cewa, kungiyar za ta gudanar da wani zaman taro kan karuwar kymar musulunci a cikin wasu kasashen yammacin turai, inda za a tattauna dalilan hakan da kuma matakan da za a dauka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bayyana cewa, kungiyar za ta gudanar da wani zaman taro kan karuwar kymar musulunci a cikin wasu kasashen yammacin turai, inda za a tattauna dalilan hakan da kuma matakan da za a dauka domin kawo karshen wannan matsala.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, Mgr Podvin babban mai magana da yawun kwamitin anyan malaman addinin kirista a kasar Faransa ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar take tafiyar da siyasarta kan mabiya addinin muslunci kuma marassa rinjaye a kasar,inda ake nuna musu banbanci na zahiri.
Ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bayyana cewa, kungiyar za ta gudanar da wani zaman taro kan karuwar kymar musulunci a cikin wasu kasashen yammacin turai, inda za a tattauna dalilan hakan da kuma matakan da za a dauka domin kawo karshen wannan matsala da take fuskantar musulmi a wannan nahiya.
807074
captcha