IQNA

Jirgin RUWa Na Tahrir Ya Kama Hanyar Kawo Karshen Killacewar Da Aka Yi Wa Gaza

19:11 - June 18, 2011
Lambar Labari: 2139706
Bangaren kasa da kasa; A kokari karo na biyu jirgin ruwa na Tahrir day a tazo daga kasar Kanada ya kama hanyarsa ta isa yankin Zirin gaza da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta Killace da zummar kawo karshen wannan ta'addanci yau sama da sheakara biyar.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; A kokari karo na biyu jirgin ruwa na Tahrir day a tazo daga kasar Kanada ya kama hanyarsa ta isa yankin Zirin gaza da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta Killace da zummar kawo karshen wannan ta'addanci yau sama da sheakara biyar.Wannan jirgin ruwa yana dauke ne da wakilan kungiyoyi da dama kuma daban daban masu rajin kare hakkin Palasdinu a a duniya da kuma yan jarida da kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa a fadin kasar ta Kanada da suka kuduri aniyar kawo karshen wannan zalunci da danniya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke nunawa wa al'ummar yankin zirin gaza da suka killace ba shiga ba bu fita a yau sama da shekaru biyu da maida yankin gidan kurkuku mafi girma a duniya da kuma sa kafa ta rushe duk wasu dokoki na ciki da na kasa da kasa da kuma yin kunnan uwar shegu kan duk wani kiran ta kawo karshen wannan killacewa. A dabra da haka hukumomi na kasa da kasa da kungiyoyi da gwamnatocin kasashen duniya bas u wani abu na azo a gani na kawo karshen lamari ko daukan mataki kan Haramtacciyar kasar ta Isra'ila.


809909

captcha