Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, pira ministan kasar Turkiya Rajab Tayyib Ardugan ya aike da wata wasika zuwa ga babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Uzma Sayyid Ali Sistani, inda ya yi tsokaci kan matsalolin kasar Bahrain, musamman ma bayan da mahukuntan kasar suka kara tsananta zaluncinsu kan fararen hula.
Dubun dubatar mutanen ne suka gudanar da zanga-zanga a jiya a sassa daban-daban na kasar Bahrain, domin nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke dauke, na yin kisan kiyashi a kan masu neman sauyi na siyasa a kasar.
Taken zanga-zangar ta jiya dai shi ne cika alkawari ga jagororin adawa da tsarin kama karya na kasar Bahrain, manufar saka wannan take kuwa ita ce kalubalantar hukuncin da kotun soji da mahukuntan kasar suka kafa take yankewa kan jagororin masu fafutukar neman sauyi, inda a cikin makonnan ta yanke hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, a kan wasu jagororin masu fafutukar su takwas, kamar yadda ta yanke wasu hukunce-hukuncen a kan wasu mutanen da suka shiga cikin zanga-zangar lumana, da hakan ya hada da hukuncin kisa da daurin shekaru a gidan kaso.
Yanke hukuncin da kotun sojin ta yi a Bahrain, ya fuskanci kakkausar suka daga al'ummomin duniya, da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kamar yadda kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi tir da hakan.
A zangar-zangar da mutanen kasar Bahrain din suka gudanar jiya, sun dora alhakin dukkanin abin da yake faruwa kansu na kisan kiyashi da cin zarafi a kan masarautar kasar, da kuma mahukuntan Saudiyya, wadanda suke da hannu dumu-dumu a cikin dukkanin abin da ke faruwa a kasar Bahrain, bisa la'akari da cewa sojojin Saudiyya ne ke jagorantar murkushe duk wata zanga-zangar lumana da cin zarafin masu gudanar da ita a kasar ta Bahrain.
814155