IQNA

Majalisar Koli Ta Mabiya Mazhabar Ahlul Bait (AS) A Masar Ta Gargadi Masarautar Bahrain

20:29 - June 25, 2011
Lambar Labari: 2144166
Bangaren kasa da kasa, babbar majalisar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar ta gargadi masarautar kasar Bahrain dangane da ci gaba da murkushe masu zanga-zangar lumanar neman sauyi, tare da kokarin mayar da hankoronsu a matsayin na bangaranci ko mazhabanci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, babbar majalisar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar ta gargadi masarautar kasar Bahrain dangane da ci gaba da murkushe masu zanga-zangar lumanar neman sauyi, tare da kokarin mayar da hankoronsu a matsayin na bangaranci ko mazhabanci da nufin kawar da hankulan al'ummomin duniya kan hakkokin mutanen kasar da aka zalunta.
Bayanin y ace matukar dai irin wannan zalunci ya ci gaba da gudana, to kuwa wannan babbar cibiya za ta kira wata gagarumar zanga-zanga a kasar Masar domin la'anatar masarautar Bahrain, tare da kiran sauran al'ummomin duniya su dauki matakan da suka dace domin ladabtar da wannan masarautar 'yar koren wahabiyawan saudiyya.
A zangar-zangar da mutanen kasar Bahrain din suka gudanar jiya, sun dora alhakin dukkanin abin da yake faruwa kansu na kisan kiyashi da cin zarafi a kan masarautar kasar, da kuma mahukuntan Saudiyya, wadanda suke da hannu dumu-dumu a cikin dukkanin abin da ke faruwa a kasar Bahrain, bisa la'akari da cewa sojojin Saudiyya ne ke jagorantar murkushe duk wata zanga-zangar lumana da cin zarafin masu gudanar da ita a kasar ta Bahrain.

Daya daga cikin jagororin masu fafutukar neman sauyi na demokradiya ta hanyar lumana a kasar Bahrai Ali Faraj, ya bayyana cewa, abin mamaki ne yadda mahukuntan Bahrain suke raya cewa a shirye suke su gudanar da tattaunawa tare da wakilan masu neman sauyi, a daidai lokacin da suke kame duk wani mai neman sauyi tare da azabtar shi, inda a cikin makonnan sun kashe akalla mutane uku a gidan kaso ta hanyar azabtarwa, ban da wadanda ba a san makomarsu ba.
Ya ce tun da al'ummar Bahrain suka fara zanga-zangar neman sauyi ba su taba jifar jami'an tsaro ko da da dutse ne ba, lamarin da ya tabbatar wa duniya cewa zanga-zangarsu ta lumana ce.

Babban abin da ya baiwa da dama daga cikin masu bin diddigin abin da ke kai da komowa mamaki shi ne, yadda kasashen yammacin turai da ke rajin kare hakkokin dan da demokradiyya suka yi shiru kan gallaza wa fararen hula masu neman sauyi da ake yi a Bahrain, a daidai lokacin da ake ganin wasu matakai akasin haka daga gare su kan Syria wadda ba su dasawa da ita, duk kuwa da cewa wasu daga cikin 'yan adawar Syria suna yin amfani da makamai ne kai tsaye wajen tunkarar gwamnati, sabanin abin da ke faruwa a kasar Bahrain.

Wannan ne ya sanya da dama daga cikin masu bin diggin lamurran suka yi amannar cewa Amurka da sauran kasashen yammacin turai, suna kare manufofinsu na siyasa ne ba hakkokin al'ummomi kamar yadda suke rayawa, domin kuwa matakin yin shiru, da nuna halin ko in kula kan zalunci da danniyar da ake yi kan al'ummar Bahrain, babban misali ne kan hakan.

814140


captcha