Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakaltoo daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, zaman taron manyan jami’an bankin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi ya kawo karshe a birnin Jidda na kasar Saudiyya, wanda ya samu halartar masana da kuma jami’an bankin daga kasashen musulmi da na larabawa inda aka gabatar da jawabai, da kuma mika makaloli.
A shafin sadarwa na yanar gizo na Times of Oman an bayyana cewa, za a sanar da sakamakon gasar hardar kur’ani mai tsarki da tajwidi da aka gudanar a kasar Oman, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur’ani ta sarki Kabus ta dauki nauyin shiryawa a birnin Maskat fadar mulkin kasar a cikin wannan wata da muke ciki rajab mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga matasana kasar Gambia da aka san su da mayar da hankali a kan lamurran da suka danganci addini, ya ci gaba da cewa da dama daga cikin masu bindiddigin lamurra suna ganin cewa bude wannan cibiya zai kara karfin matasa masu sha’awar karatun kur’ani.
Bude wata babbar cibiyar hardar kur’ani mai tsarki a birnin Crown na kasar Gambia, wanda cibiayar nan ta matasa musulmi ta kasar ta dauki nauyin ginawa da nufin bunkasa ayyukan kur’ani a kasar, musamman ma a tsakanin matasa, hakan na da daga cikin ayyukan wannan cibiya
818073