IQNA

Gasar Kur’ani Mai tsaki Ta Iran Ta tabbatar Da Matsayinta Ta Fuskacin Harda Da Karatu

14:58 - July 04, 2011
Lambar Labari: 2148772
Bangaren kasa da kasa, a kowace shekara kasar Iran tana kara fitar da matsayinta ta fuskacin harda da karatun kur’ani a matsayi na duniya a duk lokacin da aka gudanar da gasar kur’ani ta kasa da kasa da ake yi tare da halaratar sauran fitattun mahardata da makaranta na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, kowace shekara kasar Iran tana kara fitar da matsayinta ta fuskacin harda da karatun kur’ani a matsayi na duniya a duk lokacin da aka gudanar da gasar kur’ani ta kasa da kasa da ake yi tare da halaratar sauran fitattun mahardata da makaranta na duniya da take daukar nauyin gudanarwa.
a wata zantawa da wakilansa suka yi da daya dag acikin mahalarta gasar kur'ani mai tsarki ta duniya d ake gudanarwa a kasar Iran a karo na ashirin da takwas, tana samun halartar fitattun mahardata da makaranta kur'ani na duniya, wanda hakan ne ya kara ma gasar armashi matuka fiye da sauran lokutan da suka gabata.
Mahardacin kur'ani wanda yake halartar gasar daga daya daga cikin kasashen Afirka ya bayyana cewa ya ji dadin yadda ya ga gasar tana gudana abana, inda ya ce hakika ta sha banban da sauran wadanda aka gudanar a lokutan baya, kuma ya yaba da yadda masu shirya gasar suka yi iyakacin kokarinsu wajen ganin an gudanar da ita a hakan.
Daya dag acikin mahalarta gasar kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a kasar Iran a karo na ashirin da takwas, tana samun halartar fitattun mahardata da makaranta kur'ani na duniya, wanda hakan ne ya kara ma gasar armashi matuka gaya.
818721


captcha