.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wanda ya wakilci musulmin kasar Faransa agasar kur’ani ta kasa da kasa aa Tehran Ali Albinzal ya bayyana cewa, gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda a jamhuriyar musulunci ta Iran, wani babban hankoro ne na hada kan al’ummar musulmi baki daya, karba wannan kira da kuma halartar da wakilan kasashen musulmi da na larabawa suke a wannan gasa babban dalili ne kan hakan idan aka yi la’akari da tasirinsa.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na business news an bayyana cewa, pira ministan gwamnatin rikon kwarya akasar Tunisia Albaji Kaid Sabisi ya bayyana cewa suna yin matukar kokarinsu domin ganin cewa sun bunkasa ayyukan babban bankin musulunci a kasar, ta yadda zai amfanar da masu son saka hannayen jari da sauran harkokin kasuwanci.
A shafin sadarwa na yanar gizo na Times of Oman an bayyana cewa, za a sanar da sakamakon gasar hardar kur’ani mai tsarki da tajwidi da aka gudanar a kasar, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur’ani ta sarki Kabus ta dauki nauyin shiryawa a birnin Maskat fadar mulkin kasar a cikin wannan wata da muke ciki rajab mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga matasana kasar Gambia da aka san su da mayar da hankali a kan lamurran da suka danganci addini, ya ci gaba da cewa da dama daga cikin masu bindiddigin lamurra suna ganin cewa bude wannan cibiya zai kara karfin matasa masu sha’awar karatun kur’ani.
820493