Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Alwafd an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin musulmi a birnin Alkahira na kasar Masar a matsayi na kasa da kasa, wanda babbar kungiyar hadin kan malaman muslunci ta duniya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan wata da muke ciki.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lahaonline an bayyana cewa, jami'ar Azhar ta kasar Masar za ta nuna wani sabon samfuri na kundin tsarin mulkin kasar, wanda gwamnati mai zuwa za ta duba ta gani idan akwai bukar yin aiki da shi ko kuma wani bangarensa a cikin harkokin mulki a kasar da kuma siyasa ga baki daya bayan samun sauyi.
Gudanar da wannan zaman taro na tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin musulmi a birnin Alkahira na kasar Masar a matsayi na kasa da kasa, wanda babbar kungiyar hadin kan malaman muslunci ta duniya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa kamar yadda aka sanar.
821202