IQNA

8:37 - July 09, 2011
Lambar Labari: 2150843

Kungiyar Hizbullah Ta Yaba Da Furucin Shekhul Azhar Na Neman Hadin Kan Musulmi

Bnagaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta yaba da furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin mabiya tafarkin sunna da kuma mabiya tafarkin ahlul baiti.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an jaridar Qods arabi da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta yaba da furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin mabiya tafarkin sunna da kuma mabiya tafarkin ahlul baiti da aka fi sani da 'yan shi'a.

Wannan bayani da kungiyar Hizbullah ta fitar ya zo a lokacin da shehin malamin ya bayyana wa duniyar musulmi cewa 'yan shi'a musulmi ne kamar sauran musulmi, saboda haka babu wani dalili na mayar da su saniyar ware a cikin harkokin Musulunci, a lokacin da wasu mabiya tafarkin wahabiyanci ke ta kokarin fitar da mabiya tafarkin ahlul bait daga addinin Musulunci.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta bayyana furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin musulmi da cewa, wannan babban ci gaba ne aka samua acikin al'umma.

821923




captcha