Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wata gasa ta nuna samfurin tufafin muslunci ta hanyar yanar gizo internet, wanda cibiyar ta yada al’adu muslunci da ke birnin London ta kasar Birtaniya wadda ta saba gudanar dairin wadannan shirye-shirye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic Art Magazine cewa, ana shirin fara gudanar da wata gasa ta nuna samfurin tufafin muslunci ta hanyar yanar gizo internet, wanda cibiyar ta yada al’adu muslunci da ke birnin London ta kasar Birtaniya wadda ta saba gudanar da irin wadannan shirye-shirye lokuta da dama.
Labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na Bernama cewa, pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar ta Malazia.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
823747