Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro a mataki na kasa da kasa, wanda zai dubi kan matsayin al’dun muslunci a cikin rayuwar zamantakewar jama’a musamman ma a cikin kasashen musulmi da na larabawa, da wasu daga cikin kasashen nahiyar turai da suke da mazauna musulmi ko kuma suke bayar da hadin kai ga cibiyoyinsu.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
Ana shirin fara gudanar da wani zaman taro a mataki na kasa da kasa, wanda zai dubi kan matsayin al’dun muslunci a cikin rayuwar zamantakewar jama’a musamman ma a cikin kasashen musulmi da na larabawa, da wasu daga cikin kasashen nahiyar turai da suke da mazauna musulmi.
823684