IQNA

Rasuwar Abdulrahim Saih Babbar Musuiba Ce Kokarin Hada Kan Mazhabobi

18:34 - July 13, 2011
Lambar Labari: 2154226
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci na duniya ya bayyana rasuwa babban malamin kasar Masar Abdulrahim Sa'ih da cewa babbar masiba ce ga wannan kokarii na hada kan musulmin duniya baki daya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani baynai ya da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na bangaren hulad da jama'a na cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci an bayyana cewa, babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci na duniya ya bayyana rasuwa babban malamin kasar Masar Abdulrahim Sa'ih da cewa babbar masiba ce ga wannan kokarii na hada kan musulmin duniya baki daya da kuma kusanto da mazhabobinsu.

Ayatollah Tashkiri ya ce labarin rasuwar Dokta Abdulrahim Sa'ih ya girgiza dukkanin mambobin cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci, bisa la'akari da gagaruma gudunmawar da yake bayarwa wajen hada kan dukkanin al'ummar ta duniya, ta hanyar gabatar da laccoci da makaloli da ya ubuta a wannan fage.

Babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci na duniya Ayatollah Taskhiri ya bayyana rasuwa babban malamin kasar Masar Abdulrahim Sa'ih da cewa babbar masiba ce ga wannan kokarii na hada kan musulmin duniya baki daya sakamakon rasa wannan gagarumar gudunwa da yake baiwa al'ummar musulmi.

824747
captcha