IQNA

13:02 - July 14, 2011
Lambar Labari: 2154445

Kasar Indonesia Na Tunanin Kafa Cibiyar Tattaunawa Tsakanin Addinai

Bangaren kasa da kasa, kasar Indonesia ta fara tunanin kafa wata cibiya ta gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai, wadda za ta rika gudanar da harkokinta bisa ka’idoji na addinin musulunci, da nufin samun kyakkyawar fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.


Kammfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na shorouknews an bayyana cewa, kasar Indonesia ta fara tunanin kafa wata cibiya ta gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai, wadda za ta rika gudanar da harkokinta bisa ka’idoji na addinin musulunci, da nufin samun kyakkyawar fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da ma tsakanin su kansu mabiya addinin muslunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin ayyukan da fadar vatican ta saba shiryawa tun lokacin tsohon paparoma na biyu, wanda ya sa hakan ya zama wani zaman taro na shekara-shekara da ta saba gudanarwa, tare da halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen duniya, da suka hada kasashen larabawa da na musulmi baki daya.
Indonesia ta fara tunanin kafa wata cibiya ta gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai, wadda za ta rika gudanar da harkokinta bisa ka’idoji na addinin musulunci, da nufin samun kyakkyawar fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da suka hada da na muslunci kiristanci budanci da dai sauransu.
825258

captcha