Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qod Razavi an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran da ke birnin Mashhad Hujjatol Islam Qazi Askar ya bayyana cewa, an shirya wasu littafai da suke yin magana kan muhimamn ayyukan haji da ya kamata musulmi mai ziyara ya san su, wadanda aka rubuta acikin harsuna daban-daban domin amfanin maziyartan daga kasashen duniya da suke ziyartar wannna wuri mai daraja da alfarma.
Rahoton da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq akl-ausat an bayyana cewa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin London fadar mulkin kasar ta Ingila.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka shude.
826884