IQNA

Cibiyar Bunkasa Danganta Ta Musulunci A Amurka Ta Bukaci Ziyarar Masallatai

12:00 - July 21, 2011
Lambar Labari: 2157424
Bangaren kasa da kasa, cibiyar bunkasa dangantaka ta musulmi a kasar Amurka, ta bukaci wadanda ba musulmi ba da su aki ziyara amasallatan musulmi domin ganewa idanunsu irin ayyukan da musulmi suke gudanarwa a wurin.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labia day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na trouvetamosquee an bayyana cewa, cibiyar bunkasa dangantaka ta musulmi a kasar Amurka, ta bukaci wadanda ba musulmi ba da su aki ziyara amasallatan musulmi domin ganewa idanunsu irin ayyukan da musulmi suke gudanarwa a wurin da nufin kara samara da fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran al'ummar kasar.

Wasu rahotanni kuma daga kasar Syria sun habarta cewa dakarun kasar na shirin shiga yankin Bukamal da ke kan iyakar kasar da kuma kasar Iraki, biyo bayan tashe-tashen hankulan da suka faru jiya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria ya habarta cewa, wasu masu dauke da makamai da suke kiran kansu 'yan adawa a kasar Syria, sun kai hari jiya kan ofisoshin 'yan sanda da ke garin Bukamal, inda suka kasha jami'an tsaro uku kuma suka kwashe tasrin makamai da ke wurin, sun kuma ta yin harbe-harbe daga kan rufin gidaje, da sunan yunkurin kawar da gwamnatin shugaba Bashar Asad, lamarin da ya tilasta dakarun kasar suka nufi yankin a yau domin tabbatar da doka da oda, tare da kare yakokin kasar da kasar Iraki.

Kimanin watannin hudu kenan da kasar Syria take ganin tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar, tun bayan da 'yan bindiga suka fara kai farmaki kan jami'an tsaro da ma fararen hula, gwamnatin Syria ta zargi kasashen yammacin turai da wasu daga cikin kasashen larabawa 'yan koren Amurka da shirya mata makarkashiya, lamarin da ta bayyana cewa ba zai yi nasara ba.

828604
captcha