IQNA

Shekhul Azhar Ya Dauki Babban Mataki Na Yin Gyara Ta Hanyar Kare Shi'a

20:16 - July 21, 2011
Lambar Labari: 2157572
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Lebanon ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana matakin da shekhulAzhar ya dauka da cewamataki mai girma na hada kan al'ummar musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Lebanon ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana matakin da shekhulAzhar ya dauka da cewamataki mai girma na hada kan al'ummar musulmi wanda kuma wannan shi ne aikin da ya rataya kan dukkanin malaman addinin muslunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa hakika a lokacin sayyid Hassan Nasrullah yake gabatar da jawabi a gaban daruruwan 'ya'yan shahidai na gwagwarmayar muslunci a Lebanon a yakin da haramtacciyar kasar Isar'aila, ya jadda muhimmancin tsayawa kan tafarkin gwagwarmaya da neman 'yanci, kuma ya kara da cewa a yanzu kungiyar hizbullah ta kara karfi fiye da sauran lokuta.

Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Lebanon ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana matakin da shekhulAzhar ya dauka da cewamataki mai girma na hada kan al'ummar musulmi ta duniya.

828593

captcha