IQNA

Manyan Malaman Jordan Sun Haramta Nuna Fusakun Imamai Hassan Da Hussain (AS)

14:47 - July 24, 2011
Lambar Labari: 2159018
Bangaren kasa da kasa, manyan malaman kasar Jordan sun haramta suna fusakun limaman ahlul bait jikokin manozn Allah tsira da amincin su tababta a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, inda suke kallon hakan a matsayin wani aiki na assha.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, manyan malaman kasar Jordan sun haramta suna fusakun limaman ahlul bait jikokin manozn Allah tsira da amincin su tababta a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, inda suke kallon hakan a matsayin wani aiki na assha wanda wajibi ne mabiya addinin muslunci su kauce ma yin hakan.

A nata bangaren jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain (AS) a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din, wanda jami'ar take ganin cewa hakan ya sabawa koyarwar muslunci a nuna fusakun ahlul bait masu tsarki a cikin fina-finai.

Wannan jami'ar dai ita ce jami'ar musulucni mafi girma da jimawa awannan zamani, kuma bangarori daban-daban da suke kula da lamurran fatawa da sa ido kan abubuwan da ake aikatawa da matsayinsu a cikin addnin muslunci, musamman ma abubuwan da suka danganci muslunci da musulmi.

829821


captcha