Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, za a gudanar da washi na bayar da horo ga wasu 'yan kasa a mauritaniya kan yadda ake gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya, wanda zai gudana a birnin Nuwakshot na kasar Mauritania kuma zai fara daga gobe idan Allah ya kai mu, wanda wannan bababr cibiya ta yada al'adu da ilomin addinin muslunci ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Babbar manufar shirya gudanar da taron dai ita ce bayar da dama ga masu sha'awar taka gagarumar rawa wajen warware matsalolin addinai a duniya da su shiga a dama da su, domin su bayar da irin gudunmawar da suke da dauke da ita, musamman ma matasa daga cikinsu.
Gudanar da washi na bayar da horo ga wasu 'yan kasa a mauritaniya kan yadda ake gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya, wanda zai gudana a birnin Nuwakshot na kasar Mauritania kuma zai fara daga gobe a birnin tare da halartar wakilai daga kunyar da ma wasu daga cikin cibiyoyin addini na kasar.
829637