Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na allafrica an bayyana cewa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen fulatanci a tarayyar Nigeria, wanda aka nuna agarin Yola da ke jahar Adamawa da ke kasar, a lokacin da mataimakin shugaban kasar yake kai wata ziyara a can jahar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a lokacin da aka gudanar da wani bababn taro na nuna wannan kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin haershen fulatanci a garin Na Yola, mataimakin shugaban kasar Namadi ya sambo ya gabatar da jawabi, wanda a cikinsa yake cewa wajibi ne kan dukknin musulmi su yi aiki da koyarwar kur'ani mai tsarki.
Nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen fulatanci a tarayyar Nigeria, wanda aka nuna agarin Yola da ke jahar Adamawa da ke kasar, a lokacin da mataimakin shugaban kasar yake kai wata ziyara a garin, hakan na tabbatar da irin gagarumin ci gaban da aka samu net a fuskacin ayyukan kur'ani mai tsarki a kasar.
831789