IQNA

Kwamitocin Bayar Da Agaji Na Kungiyar Kasashen Musulmi Sun Gudanar Da Zama

15:12 - July 30, 2011
Lambar Labari: 2161882
Bangaren kasa da kasa, mambobin kwamitocin bayar da agaji na kasashen musulmi sun gudanar da wani zama domin tattauna hanyoyin da za su bi domin bayan da taimako ga masu bukata a kasar Somalia, bisa la’akari da a halin ake ciki a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo oci cewa, mambobin kwamitocin bayar da agaji na kasashen musulmi sun gudanar da wani zama domin tattauna hanyoyin da za su bi domin bayan da taimako ga masu bukata a kasar Somalia, bisa la’akari da a halin akae ciki a kasar ta Somalia, musamman ma kan batun yunwa da farin da ake fuskanta.
Cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya, kuma wannan shi ne karon farko da za agudanar da irinsa.
A yayin gudanar da zama masana da malaman jami’oi za su halarta kuma za su gabatar da laccoci ga mahalrta taron, daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai nazari kan matsayin sharia a cikin addinin muslunci, da kuma yadda wannan addini mai tsarki yake kallon rayuwar zamantakewa ta jama’a.
Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya a karon farko.
833348
captcha