IQNA

11:48 - July 31, 2011
Lambar Labari: 2162515

An Fara Gudanar Da Shirin Bayar Da Horo Ga Daliban Kur'ani 'Yan Shia A Saudiyya

Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan karatun kur'ani mai tsarki da hakan ya hada da harda da kuma karatu gami da sanin ka'idojin karatun kur'ani wato ilimin tajwidi kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta rasid an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan karatun kur'ani mai tsarki da hakan ya hada da harda da kuma karatu gami da sanin ka'idojin karatun kur'ani wato ilimin tajwidi kamar yadda aka saba yi a kowace shekara a yankin katif wanda mazauna cikinsu akasarinsu mabiya tafarkin iyalan gidan manz allah ne.

Wani labari day a nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Benama an bayyana cewa, a dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar Malazia, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu a gasar da ake gudanarwa a karo na hamsin da uku.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin wadanda suka kai ga wannan mataki hard a 'yan kasashen Sudan, Viatnam, Thailand, Senegal, Srilanka da dai sauransu, lamarin day a bayar da matukar mamaki, domin babu ko daya daga cikin kasashen da ta samu kaiwa zuwa ga mataki na karshe a gasar.

A dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar Malazia, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu domin neman kaiwa ga mataki na karshe a wanna gasa.
833955
captcha