IQNA

An Nuna Wasu Daga Cikin Littafan Addini Da Aka Tarjama A Cikin Turanci

13:36 - August 01, 2011
Lambar Labari: 2163372
Bangaren kasa da kasa, an nuna wasu daga cikin littafan da aka tarjama a cikin harshen turancin ingilishi domin amfanin masu Magana da wannan harshe a cikin kasashen musulmi da kuma kasashen turai, daga cikin littafan kuwa har na addu'oi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an nuna wasu daga cikin littafan da aka tarjama a cikin harshen turancin ingilishi domin amfanin masu Magana da wannan harshe a cikin kasashen musulmi da kuma kasashen turai, daga cikin littafan kuwa har na addu'oi da suka hada da mafatihul jinan da kuma sahifat sajjadiyya, wanda ya hada addu'oi da daman a Imam Aliyu Bin Hussain zainul Abidin (AS).

Baynain ya ci gaba da cewa a wanna taro na baje kolin kur'ani mai tsarki a karo na goma sha tara 19 da ake gudanarwa abirnin Teran, an nuna irin wadannan litatfai wadanda suka danganci ayyuka na kur'ani mai tsarke da ake gudanarwa airin wadannan wurare da kuma sabbin na'urori masu kwakwalwa da aka tsara su kan kur'ani.

An kuma nuna wasu littafan na daban, kamar littafin nahujul balagha da aka tarjama a cikin harsuna daban-daban musamman a cikin harshen turanci, wanda ya hada mujalladai da dama, taron baje kolin dai yana samun halartar cibiyoyin addini da dama.

Nuna wasu daga cikin littafan da aka tarjama a cikin harshen turancin ingilishi domin amfanin masu Magana da wannan harshe a cikin kasashen musulmi da kuma kasashen turai, daga cikin liffan kuwa har na addu'oi kamar yadda rahoton ya tabbatar.
834298
captcha