IQNA

14:15 - August 03, 2011
Lambar Labari: 2164752

Wurin Ajiye Kayan Tarihi Na Imam Hussain (AS) Ya Shiga Jerin Irinsa A Iraki

Bangaren kasa da kasa, wurin ajiye kayan tarihi na Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma akasar Iraki, ya shiga cikin jerin muhimman wuraren kayan tarihi na kasar Iraki akmar yadda hukumar kula da kayan tarihi ta kasar ta sanar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, sabon wurin ajiye kayan tarihi na Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma akasar Iraki, ya shiga cikin jerin muhimman wuraren kayan tarihi na kasar Iraki akmar yadda hukumar kula da kayan tarihi ta kasar ta sanar daga cikin wannan shekara da muke ciki.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin ministocin gwamnatin Iraki ne suka amince da hakan, inda aka kara da hubbaren Abul Fadl Abbas (AS) da kuma hubbaren mai tsarki na Imam Hussain (AS) wadanda dukakninsu suke birnin na karbala mai alfarma, masu kula da hubbarorin sun dauki alkawalin bayar da dukkanin hadin kai da ake bukata ta wannan fuska.

Wannan wurin ajiye kayan tarihi da suka danganci Imam Hussain (AS) da sahabbansa (RA) an fara gudanar da aikinsa ne tun kimanin shekaru biyu da suka gabata, kuma acikin watan da ya kare ne aka bude shi a hukumance, tare da halartar wasu daga cikin jami'ai na kasar.

Wurin ajiye kayan tarihi na Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma akasar Iraki, ya shiga cikin jerin muhimman wuraren kayan tarihi na kasar Iraki akmar yadda hukumar kula da kayan tarihi ta kasar ta sanar a cikin wannan mako.

836010

captcha