IQNA

Gabatar Da Mahanga Kan Sahihin Karatun Kur’ani A Cikin Salla A Baje Koli

20:10 - August 06, 2011
Lambar Labari: 2166061
Bangaren kasa da kasa, gabatar da mahanga kan sahihin karatun kur’ani mai tsarki a cikin salla, wanda jami’ar bincike kan imlmomi ta harhada tare da mika shi a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha tara a birnin Tehran.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gabatar da mahanga kan sahihin karatun kur’ani mai tsarki a cikin salla, wanda jami’ar bincike kan imlmomi ta harhada tare da mika shi a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha tara a birnin Tehran kamar dai yadda madaba’antu da cibiyoyin kur’ani mai tsarki suka saba gabatarwa.
A wani labarin na daban kuma ya nakalto wani rahoto da aka buga a shafin yanatr gizo na jaridar Al-riyad da ake bugawa a kasar saudiyya, da ke cewa daliban makarantun sakandare ne da sukahardace kur’ani mai tsarki za agirmama ayankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya, wanda mafi yawan mazauna cikinsa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ne a wannan rana.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke karawa da juna domin nuna irin baiwar da Allah madaukakin sarki ya yi musu.
Makarnaci ya samu kyakkyawar karbuwa daga su kansu makaranta da suke halartar wannan gasa daga kasashen duniya daban-daban musamman na musulmi da na larabawa, kamar yadda kwamitin shirya gasar ya nuna matukar gamsuwa da yadda yake yin amfani da salo na musamman wajen karanta littafin Allah mai tsarki.
837549

captcha