IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani Ta Kurame A Kasar Kuwait

10:53 - August 09, 2011
Lambar Labari: 2167695
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta kurame a kasa Kuwait a babban otel din nan Raya da ke kasar wanda ke samun samun halartar mahardata daga kasashe daban-daban da suke gudanar da gasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta kurame a kasa Kuwait a babban otel din nan Raya da ke kasar wanda ke samun samun halartar mahardata daga kasashe daban-daban da suke gudanar da gasar kamar dai yadda aka shirya.

Daya daga cikin masu shirya wannan gasaAbdullah Jadan ya bayyana cewa, ya zuwa kasashe goma sha daya ne daga cikin kasashen musulmi suka turo wakilansu zuwa wannan gasa, kuma za a ci gab ada gudanar da ita kamar yadda aka shirya a cikin wannan wata na ramadana mai alfarma.

Daga cikin kasashe har da Morocco da Lebanon, Jordan Masar yeman da dai sauransu da kuma wasu daga cikin kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya da suka nuna matukar sha'awarsu kan wannan gasa.

Fara gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta kurame a kasa Kuwait a babban otel din nan Raya da ke kasar wanda ke samun samun halartar mahardata daga kasashe daban-daban da suke gudanar da gasar na matsayin wata babbar nasar ga cibiyar shirya gasar kur'ani ta kasar Kuwait, bisa la'akari da cewa wannan shi ne karon farko da ake shirya irin wannan gasa.

839229
captcha