IQNA

Daren Yau Ne Za A Kammala Gasa gasar Karatu Da Hardar Kur'ani A Dubai

12:35 - August 11, 2011
Lambar Labari: 2168896
Bangaren kasa da kasa, a cikin daren yau ne za a kammala gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai an aksar hadaddiyar daular larabawa, inda mahardata kur'a takwas za su kara da juna.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Darul khalij da ake bugawa a kasar hadaddiyar daular larabawa cewa, a cikin daren yau ne za a kammala gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai an aksar hadaddiyar daular larabawa, inda mahardata kur'ani takwas za su kara da juna kamar dai yadda cibiyar shirya gasar ta ambata.
Dole ne mutum ya saka rayuwarsa bisa tsari, domin ubangiji bai bar lamarin bayanisa a sake ba babu tsari, ta yadda bayinsa za su ci gajiyar rayuwarsu ta duniya a rayuwa ta har abada, haka nan mutumzai iya cin ribar rayurwa ne idan ya tsara ta kan biyayya ga umurnin Allah, tare da aikata kyawawan ayyuka, da tsara loktansa na ibada da ayyuaknsa na neman halas domin ya samu abin da zai rayu da shi da iyalansa.
Kyakkyawan aiki a koda yaushe hankali da shari’a suke yin umurni da shi, domin kuwa shi ne ke ga ma’abocinsa zuwa ga samun taqawa, ba hada ayyuka n shirme da ayyuka na kwarai, domin kuwa sabin na kwarai ba su kai ma’abocinsu ga taqawa, alhali kur’ani mai tsarki ya gaya mana cewa: Allah yana karbar ayyuka ne kawai daga masu taqawa, wadanda suka yi aiki dominsa, domin samun yardarsa, ba wai domin haka suka ga mutane na yi, ba domin haka suka tashi suka ga a gidansu ana yi ba.
840647
captcha