IQNA

Zaman Tattauanawa Kan fadakar Musulunci A taron baje Koli

16:12 - August 13, 2011
Lambar Labari: 2169899
Bangaren kasa da kasa, Munafunci wata rashin lafiya ce da ke cutar da dan adam a cikin dukkanin lamurransa na rayuwarsa ta zamnatakewa, wanda idan ma’abocinsa bai iya shawo kan wannan matsalar ba, a cikin kankanin lokaci zai cutar da dukaknin sauran mutanen da yake rayuwa tare da su.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daga cikin abubuwan da munafunci ke haifarwa har da riya da nuna fuskoki daban-daban a cikin al’umma, tare da yaduwa fasadi da barna.
Munafuki ya san cewa baya aiki da koyarwar addini da umurninsa, haka nan kuma yan ason hana dukkanin mumunai yin aiki da koyi da addini a cikin lamurransu na rayuwa, a kan haka ne yake yin izgigili ga umurnin Allah, haka nan kuma baya bayar da muhimmanci ga duk wani aikin addini.

Kur’ani mai ttsarki ya yi nuni zuwa ga wasu daga cikin soffofin munafukai a cikin suratul munafikin, da kuma surat tauba, irin yadda suke gudu a lokacin yaki da makiya addnin muslunci, domin su karya gwiwar muminai su sanya su su yi rauni, ko kuma a lokacin da ake bayar da gudunmwa wajne taimakon addinin Allah, sai su rika yin izgili ga masu bayar da kudade, duna cewa wadannan ‘yan kudin ba su da wata kima, domin kawai su hana musulmi yin aikin ibada.

Munafunci shi ne tushen duk wata barna a cikin al’umma, ammam mai irin wannan dabi’a idanunsa makance suke ba ya ganin gaskiya balantan aya bi ta, kuma a lokaci guda baya ganin barnan da yake kuma yake watsawa cikin mutane.

A maimakon haka ma munafukai suna ganin su ne kan sahihin tafarki, inda suke ganin cewa kawo cikas ga aikin jihadi wani kokari ne na hana zubar da jini, duk kuwa da cewa rashin yin hakan shi ne zai karfafa makiya da kafirai wajen yin dirar mikiya kan addini da mabiyansa. 841730
captcha