IQNA

Goyon Bayan Da Ira Take Baiwa Hizbullah Babban Abin Alfahari Ne Ga Kungiyar

10:06 - August 14, 2011
Lambar Labari: 2170164
Bangaren kasa da kasa, mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Shikh Na'im kasim ya bayyana goyon bayan da jamhuriyar muslunci take baiwa kugiyar da cewa babban abin alfahari da ma sauran kungiyoyin da Iran take marawa baya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga tashar talabijin din Almanar ta kasar Lebanon cewa, mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Shikh Na'im kasim ya bayyana goyon bayan da jamhuriyar muslunci take baiwa kugiyar da cewa babban abin alfahari da ma sauran kungiyoyin da Iran take marawa baya daga cikin kungiyoyin gwagwarmaya da suka hada da Hamas da kuma Jihadul-islami.

Ya ci gaba da cewa, abin mamaki ne yadda wasu suke zargin cewa wai kungiyoyin gwagwarmaya suna yi wa kasashe irin su Iran da Syria aiki ne, wanda kuma dukaknin abin da wadannan kungiyoyin suke yi amfanin hakan yana komawa ga al'umma ne, duk kuwa da cewa abu ne sananne wadanda suke irin wadannan maganganu ba su fatan alkhairi ga wannan al'umma.

Bayanin ya ci gaba da cewa mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Shikh Na'im kasim ya bayyana goyon bayan da jamhuriyar muslunci take baiwa kugiyar da cewa babban abin alfahari da ma sauran kungiyoyin da Iran take marawa baya a yankin, ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan batun gwagwarmaya da makiya addini.

Kasashen yammacin turai suna ci gaba da matsin lambarsu kan kasashen Iran da Syria babu kakkautawa, domin ganin sun karya lagon masu fafutukar neman samun 'yanci daga sabon mulkin mallakar kasashen yammacin turai da yahudawan sahyuniya.
842088
captcha