IQNA

10:52 - August 15, 2011
Lambar Labari: 2170894

Taro Mai Taken Kur'ani Littafin Fadaka A Baje Kolin Kur'ani Na Duniya

Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro mai taken kur'ani littafin fadaka a wurin bae kolin kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, tare da halartar masana na cikin gida kuma na kasashen ketare.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro mai taken kur'ani littafin fadaka a wurin bae kolin kur'ani na duniya da ake gudanarwa tare da halartar masana na cikin gida kuma na kasashen ketare wurin gudanar da baje koli na kasa da kasa.

A bangare guda wani rahoton ya ce shugaban kwamitin tsaro da kuma siyasar harkokin wajen Majalisar dokokin kasar Iran Ala'eddin Bourjari, ya ce sojojin kare juyin musuluncin na kasar sun cafke mataimakin shugaban kungiyar 'yan tawaye ta Turkiyya wanda yake boye a cikin tsaunukan qandil kusa da iyakar Turkiyya da kuma Iran.

Bourjadi ya bayyana hakan ne a jiya ga manema labarai a nan birnin Tehran, yana mai cewa kama mataimakin shugaban kungiyar ta wata babbar nasara ce da kuma kwazo da dakarun kare juyin musulunci na kasar suka nuna, wadanda ya ce har kullum suke a shirye domin kare iyakokin kasar.

Tun a shekarar ne dai a karkashin jagorancin shugabanta wanda shi ma aka cafke wato Abdallah , kungiyar ta soma yin amfani da makamai domin kai farmaki a kan jami'an tsaro da kuma sauran muhimman wurare a cikin kasar.

843265

captcha