IQNA

13:55 - August 17, 2011
Lambar Labari: 2172698

Gwagwarmaya Ce Kawai Za Ta Kawo Karshen Mamayar Yahudawan Sahyuniya

Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta jaddada wajabcin ci gaba da yin gwagwarmaya domin kawo karshen ayyukan mamaya na yahudawan sahyuniya a cikin yankunan palastinawa.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alalam an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta jaddada wajabcin ci gaba da yin gwagwarmaya domin kawo karshen ayyukan mamaya na yahudawan sahyuniya a cikin yankunan palastinawa da suke gabacin birnin qods da sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Madaukakin sarki ya halicci mutum, ya kuma saka shi a bayan kasa, ya sanya wasu abubuwa da dan adam yake bukata domin ci gaba da wannan rayuwa, domin wanzur irin mutum yana bukatar mata da 'ya'ya, domin jin dadin rayuwrsa da biyan bukatunsa na yau da kullum yana bukatar kudi.

Yana bukatar abin hawa da tufafi da dai sauran abubuwa na bukatuwar dan adam na larura. Mutum yakan so wadannan abubuwan kamar yadda Allah ya sanya sonsu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma yakan so su fiye da kima, har ma mutum kan iya sanya su tamkar su ne manufar rayuwarsa, ya fifita son mata da 'ya'yansa da dukiyarsa fiye da komai na duniya, har ma da ibadar Allah madaukakin sarki, alhali kuwa ba su ne manufa ta rayur dan adam ba,

Domin kuwa su ma masu karewa ne a nan gidan duniya, kuma dayan biyu, kodai mutum ya barsu, ko kuma su su bar shi, domin kuwa makomar kowa da komai na wajen Allah madaukakin sarki. Idan mutum bai kyautata ayyukansa ba, babu ko daya daga ckin wadannan abubuwan da zai amfane shi a lahira. 844445
captcha