Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, daruruwan matasan kasar Masar ne suka gudanar da wata zanga-zanga a jiya agaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar domin yin Allawadai da kasha jami'an tsaron kasar da ta yi biyo bayan harin da wasu daga cikin masu gwagwarmaya suka kai kansu.
Bayanin ya ci gaba da cewa daruruwan mutane ne suka taro a gaban ofishin jakadancin HKI da ke birnin Al-kahira a yau jumma'a, inda suka bukaci gwamnatin sojojin kasar Masar ta kori jakadan Isra'ila da ke kasar sandaiyyar hare haren da HKI ta kai a kan iyakar kasashen biyu wanda ya kai ga mutuwar sojojin kasar akalla guda hudu.
A halin yanzu dai Janar Sami Anan wani komandan sojojin kasar ta Masar yana kan hanyarsa ta zuwa yankin Sina inda abin ya faru don ganewa idanunsa irin barnan da hare haren da jiragen yakin Isra'ila suka yi a yankin a jiya aljamis.
Har'ila yau a jiya din jiragen yakin Isra'ila sun kai hare hare a yankin Gaza inda suka kashe Palasdinawa 7 daga cikinsu har da wani yaro dan shekara 9 a duniya.
Gwamnatin Isra'ila dai ta kai hare haren nan ne bayan wani harin konan bakin waken da aka kaiwa yahudawa a cikin kasar Palasdinu da take mamaye da shi, inda 6 daga cikinsu suka halaka wasu kimani 12 kuma suka ji rauni.
846593