IQNA

A Daren Yau Mahdi Muhaqqik Zai Gabatar Da Jawabi A Gaban Taron baje koli

17:13 - August 23, 2011
Lambar Labari: 2175718
Bangaren kur'ani, a daren yau daya daga cikin fitattun malamn addinin muslunci zai gabatar da wani jawabi a wajen taron baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gabatarwa a karo na goma sha tara da zai hada da tasirin rubuta wajen yada manufar kur'ani.



Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar day a nakalto daga shafin sadarwarsa an bayyana cewa, Mahdi Muhaqqiq a daren yau daya daga cikin fitattun malamn addinin muslunci zai gabatar da wani jawabi a wajen taron baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gabatarwa a karo na goma sha tara da zai hada da tasirin rubuta wajen yada manufar kur'ani a gaban daruruwan mahalarta.

Bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurnin manzon Allah a lokacin yakin Uhud, wasu daga cikinsu zuciyarsu ta raunana, sai suka fara jin tsoro, suka fara nuna damursu da kaduwarsu a fili, suna tambayar cewa yaya makomarsu za ta kasance idan kafirai suka yi nasara a kansu.

Kenan za su kaskanta. A cikin nassin wannan aya mai albarka Allah madaukakin sarki yana sheda ma manzonsa (SWA) cewa nasarar da kafirai suka samu a Uhud bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurninsa, ba nasara ce ba ga kafirai, haka nan kuma ba wata daukaka ba ce balantana su daga ma musulmi kai, hakan lamari ne kawai da zai kara saka su cikin halakar kafirci da shirka.

Suna cikin hasarar duniya da kuma hasarar lahira. Haka nan kuma kafircin wadannan mushrikai ba zai cutar da Allah madaukakin sarki da komai ba. Maimakon haka ma su ne suke cutuwa da kafirci da shirkarsu, kuma su koma zuwa ga Allah su shiga azaba mai radadi.

847754
captcha