IQNA

Mai Bayar Da Fatawa Na Saudiyya Ya Kore Shakku Kan Ganin Wata

17:56 - September 03, 2011
Lambar Labari: 2180626
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa a kasar Saudiyya Abdulaziz bin Abdulalh Ali-sheikh yak ore jita-jitar da aka yi ta yadawa kan batun shakkun da ake cewa an yi dangane da ganin watan shawwal na bana.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na emaratalyaum an bayyana cewa babban mai bayar da fatawa a kasar Saudiyya Abdulaziz bin Abdulalh Ali-sheikh yak ore jita-jitar da aka yi ta yadawa kan batun shakkun da ake cewa an yi dangane da ganin watan karamar salla na wannan shekara.

Malamin tare da babban mai bayar da fatawa na kasar Ali Jum'a sun fitar da banin ne na hadin gwiwa dake kore duk wata jita-jita da ake yadawa kan batun rashin ganin watan karamar salla na bana, inda wani dan salafiya da ke bin tafarkin wahabiyanci ya bayyana cewa an yi salla ne bisa dogaro da ganin wata amma kuma a cewarsa ba wata ne ba kwallon duniya na zuhal ne aka gani.

Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin bayanan da aka bayar dangane da ganin watan sun dogara bisa hujjuji na ilimi, tare da bayyana wa sauran mutane da suka yi salla da kada su rudu da wannan batu marassa tushe balanta makama.

Mai bayar da fatawar a kasar Saudiyya Abdulaziz bin Abdulalh Ali-sheikh tar da mai bayar da fatawa na Masar duk sun ya kore jita-jitar da aka yi ta yadawa kan batun shakkun da ake cewa an yi dangane da ganin watan shawwal na bana da cewa aikin shaidan ne kawai.

853216

captcha