IQNA

Birnin Sirt Shi Ne Sabuwar Fadar Mulkin Kasar Yadda Gaddafi Ya Sheda

17:54 - September 03, 2011
Lambar Labari: 2180631
Bangaren kasa da kasa, shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi ya bayyana a cikin wani bayani da aka nada ta hanyar kaset cewa, birnin Sirt shi ne babban birni kuma fadar mulkin halastacciyar gwamnatin Libya.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yaum al-sabi cewa, shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi ya bayyana a cikin wani bayani da aka nada ta hanyar kaset cewa, birnin Sirt shi ne babban birni kuma fadar mulkin halastacciyar gwamnatin Libya da ke karkashin ikonsa da mabiyansa.
Tun bayan da aka shiga cikin wani yanayi a kasar ta Libya dai babu labarin Mu'ammar Gaddafi, amma yanzu haka dai birnin Tripoli ya zama wata madaddala ta 'yan bindiga da suke samun goyon bayan kasashen yammacin turai kai tsaye, bayan da Gaddafi da magoya bayansa da suke dauke da makamai suka bata bat daga birnin.
Ministan cikin gida na hukumar wucin gadin kasar Libya Ahmed Darrad ya ce sun sanar da mayakan da suka kawo dauki daga wasu garuruwa zuwa birnin Tripoli domin kifar da gwamnatin Mu'ammar Kaddafi da su koma gida.Darrad ya ce yanzu kam an 'yantar da birnin Tripoli kuma daga ranar gobe Asabar adadi mai yawa na jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda za su koma bakin aikinsu.
Darrad ya kara da cewa 'yan juyin juya halin na birnin Tripoli za su iya kare birninsu.
Wannan kira dai yana a matsayin kokari na farko da sabbin shugabannin kasar ta Libya ke yi na kauce wa sabanin da ake tsoron faruwarsa tsakanin sabbin shiga juyin juya hali na Tripoli da kuma gogaggun 'yan tawayen da suka shigo birnin daga wajensa.

A daya bangare kuwa Majalisar riko ta kasar ta Libya ta ce a cikin watanni 20 masu zuwa ne za'a kammala shimfida demokradiyya a kasar, wato daga aikin rejistar masu zabe, har zuwa zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar dokoki a kasar.
853174

captcha