IQNA

Kungiyar Hadin Kan Musulmi Za Ta Gudanar Da Zama Karo Na Ashirin Da Bakwa

18:54 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181212
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi na shirin gudanar da zama karo ashirin da bakwai domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci kasashen musulmi musamman ma na larabawa daga cikinsu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo sesric cewa kungiyar hadin kan kasashen musulmi na shirin gudanar da zama karo ashirin da bakwai domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci kasashen musulmi musamman ma na larabawa daga cikinsu da suka fama da tashin hankali a cikin shekarar nan.

Yan'uwa masu girma cikin wadannan silsila na shirye-shiryen da za mu gabatar muku da su za mu gabatar muku da wasu ma'anoni ne na ayoyin Alkur'ani mai girma da irin sakonnin da ke cikinsu don ku din nan masu karatu da saurare ku sami damar tsara rayuwar ku gwargwadon koyarwar Alkur'ani don sama wa kanku sa'ada, sannan kuma ku amfanar da rayuwar da karatun ayoyin Alkur'ani mai girma.

Kamar yadda muka sani, yana da surori 114 ne sannan kuma kowace sura tana da wasu ayoyi a cikinta. Alkur'ani dai ya fara ne da surar da ake kiranta da sunan 'Mabudin Littafi' wacce aka fi saninta da Suratul Hamd. Daga cikin muhimmancin da wannan sura wacce take da ayoyi bakwai take da shi, shi ne cewa a kowace rana wajibi ne a karanta alal akalla sau goma yayin salloli biyar na rana, wanda idan ba a karanta ta ba, to salla ta baci.

Wannan sura wacce ita ce mafarin littafin Allah ta fara ne da wata aya wacce duk wani aikin da mutum ya fara da ita to kuwa karshen aikin zai zamanto mai kyau, domin kuwa ayyuka masu kyau sun e abin alfahari da su ranar kiyama.

853574

captcha