IQNA

Kasashen Turai Na Son Shigewa Gaba A yunkurin Al’ummomin Larabawa

20:23 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181241
Bangaren siyasa da zamantakewa, shugaban cibiyar bunkaka harkokin al’adu da ilmomin musulunci ya yi nuni da cewa, kasashen yammacin turai suna hankoron ganin su ne suke juya al’ummomin larabawa da kuma juyin da suke yi a cikin kasashensu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar da aka mabata inda shugaban cibiyar ta bunkaka harkokin al’adu da ilmomin musulunci ya yi nuni da cewa, kasashen yammacin turai suna hankoron ganin su ne suke juya al’ummomin larabawa da kuma juyin da suke yi domin kawo karshen mulkin kama karya da fir’aunanci.
Muhammad Baqer Khoramshad ya bayyana hakan ne a lokacin da ake shirin fara gudanar da hudubar sallar juma’a a birnin Tehran, inda ya yi wata yar takaitacciyar lacca kan wannan batu da ma wasu batutuwa da suka danganci makircin da ake kitsawa kasashen musulmi daga kasashen yammacin turai.
Ya ce dole ne al’ummomin kasashen larabawa su kasance cikin fadaka kan abubuwa da ke kai suna komowa domin kaucewa fadawa cikin tarkon da wadannan kasashen suke shiryawa kan al’ummar musulmi a wannan zamani.
Dangane da tasirin da juyin juya halin jamhurin musulunci ta Iran ya yi kuwa, ya bayyana cewa duk wannan yunkurin da muke gani ya samu asali ne daga kasar Iran, inda al’ummarta suka tashi a cikin shekaru talatin da uku da suka gabata suka kawo karshen mulkin tagutanci.
853431
captcha