IQNA

18:13 - September 05, 2011
Lambar Labari: 2181911
Bangaren siyasa da zamantakewa, mabiya addinin muluslunci sun zama abin yankawa ahannun mabiya addinin kirista da suke tsattsauran ra'ayi a tarayyar Nigeria a garin Jos da ke tsakiyar kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Mirror da ake bugawa a Nigeria cewa, mabiya addinin muluslunci sun zama abin yankawa ahannun mabiya addinin kirista da suke tsattsauran ra'ayi a tarayyar Nigeria a garin Jos wanda ya saba da ganin irin wadannan tashe-tashen hankula.

Wani rahoton kuma yana cewa yan bindiga dadi sun harbe wani malamin addinin musulunci a garin maiduguri da ke arewacin Najeriya a jiya lahadi.
Wani jami'in 'yan sanda a garin na maiduguri ya fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa: "An kashe wani limami da ake kira malam Dala a kofar gidansa da safe a unguwar Zinary da ke cikin maiduguri.

Jami'in 'yan sandan ya ci gaba da cewa, wasu mutane biyu da su ke cikin mota sun tsaya a bakin gidan malamin sannan su ka bude wuta akansa daga kusa, bugu da kari jami'in 'yansandan ya ce babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kashe malamin, sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin hakan.

Birnin maiduguri dai yana fama da fadace-fadace tsakanin 'yan kungiyar da ake kira Boko-Haram da kuma sojoji, duk kuwada cewa mutane sun da shedun gani da ido sun tabbatar cewa wannan dakarun gwamnati suna kasha fararen hula.

854037


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: