Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da ke cwa, bababn jami'I mai kula da harhada bayanai na asiri a jamhuriyar musulunci ta Iran Haidar Moslehi ya gabatar da jawabi a gaban wani taro na Iraniyawa mazauna kasashen ketare da yake da dangantaka da al'adu da suka hada dukkanin al'ummar wannan kasa aduk inda suke a duniya.
Wannan dai shi ne karo na tara da ake gudanar da irin wannan taro, wanda ya tabbatar da cewa hakika iraniyawan suna da kyakwar alaka da kasarsu da kuma al'adunsu, a nasa banagren babban mai baiwa jagoran juyin juya hali shawarwari harkokin siyasa Ali Akbar wilayati ya gabatar da jawabi a wurin.
Babbar manufar taron dai it ace kara karfafa gwiwar Iraniyawan da suke kasashen ketare wajen yin riko da koyarwar musulunci wadda juyin juya halin kasarsu ya ginu a kasansa, tare da kara samun fadaka dangane da abubuwan da ke faruwa acikin kasashen larabawa.
855014