IQNA

Shekhul Azahar Ya Haramta Taron Sulhu Na Duniya A Jamus

18:25 - September 06, 2011
Lambar Labari: 2182592
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami'ar Azhar ya haramta halartar taron sulhu na duniya da za a gudanar a kasar Jamus saboda halartar wani khakham na yahudawan sahyniyan Isra'ila a wajen taron.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sbi ta kasar Masar an bayyana cewa, Ahmad Tayyib babban malamin jami'ar Azhar ya haramta halartar taron sulhu na duniya da za a gudanar a kasar Jamus saboda halartar wani khakham na yahudawan sahyniyan Isra'ila a wajen taron a birnin Monekch.

Malamin ya ce labaran da aka yi ta yadawa kan cewa zai halarci taron na sulhu na duniya babu gaskiya a cikinsu, domin kuwa shi ba zai halarci taron wani malimin yahudawan sahyuniya daga haramtacciyar kasar yahudawa zai halarta ba.

Mutane sun kasu kashi uku ta fuskar aiki da manufar aikin nasu, kashi na farko su ne masu yin aiki saboda Allah, ba son wani yasan abin da suka yin a alkhairi in ba Allah, domin kuwa saboda shi suka yi. Kashi na biyu kuma su ne wadanda suke yin aikin alhairin, amma kuma a lokaci guda suna mutane su san sun yi domin a yaba musu, su ne ake kira masu aikin riya.

Kashi na uku kuma su ne wadanda ba sa yin aikin alkhairi, amma kum suna son yabo daga mutane, wannan aya ta zargi kashi na biyu da na uku, tare da bayyana su a matsayin wadanda za su tashia tutar babu, maimakon haka ma za su hadu da fushin ubangiji a ranar kiyama.

854876


captcha