Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya samu wani labari ta hanayar yanar gizo USIM da ke cewa, yanzu haka an fara shirin gudanar da wani zaman taro a cikin ranakun sha biyu da sha uku na watan mai kamawa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia a matsayi na kasa da kasa, kan shugabancin musulmi na duniya baki daya.
Daya daga cikin abubuwan da kur'ani mai tsarki ya kebanta da su shi ne, kiran musulmi zuwa ga tunani a cikin ayoyin Allah da ke cikin halittunsa, domin kara samun sakankancewa da ubangiji. Imani yana da abubuwan da suke kara karfafa shi tare da kai shi zuwa ga babban matsayi, baya ga sauran ayyuka na ibada da Allah ya farlanta.
Da kuma wadanda aka so yi na mustahabbi, tare da aikata umurnin Allah da hanuwa da haninsa a cikin dukaknin lamurra, yin tunani kan halittar sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, da kuma yadda Allah yake sarrafa dare da rana sauran ayoyin ubangiji, hakan yana matsayin ibada ne, kuma yana kara karfafa imanin musulmi.
An bayyana wadannan ayoyin biyu daga cikin ayoyin da ake son mutum ya karanta kafin ya fara sallar dare (kiyamullail) domin kuwa suna tuna mutum mutum da kudirar Allah, da kara sanin matsayin girmansa.
854710