Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalt daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Ahram cewa, gungn matasan kasar masar amsu juyi sun gufanar da wata zangazangar nuna kin amincewa da dawo da dokar t abaci da ta haramta gudunar da duk wani juerin gwano a fadin kasar baki daya kamar dai lokacin mulkin tsohon shugaban kasar.
Rahoton ya nuni da cewa a daya bangaren Jakadan kasar Siriya a kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Yusuf Ahmad ya yi watsi da sanarwar bayan taron ministocin kasashen larabawa da suka fitar a jiya talata bayan taron da suka gudanar a helkwatar kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar.
Wakilin kasar Siriyan ya bayyana wannan sanarwar a matsayin alamar adawa da kasar Siriya sannan kuma wani kokari na yin kafar ungulu ga kokarin da babban sakataren kungiyar ya faro wajen magance matsalar da ta kunno kai a kasar Siriyan.
Jakada Yusuf Ahmad ya kara da cewa tun farko wasu gwamnatocin kasashen larabawan da kafafen watsa labaransu sun ta kokarin wajen ganin wannan kokarin bai yi nasara ba, yana mai tuhumarsu da gudanar da abubuwan da manyan kasashen duniya suke son gudanarwa a kokarin da suke yi na kulla wa kasar Siriyan makirci da kifar da gwamnatin kasar.
Daga karshe dai jakadan kasar Siriya ya ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da gudanar da shirin sauyi da ta kaddamar a kasar ba tare da la'akari da irin wadannan makirce-makircen da ake kulla mata ba.
860278