IQNA

An Bukaci Hana Na Kusa Da Mubarak Tsayawa Takara A zabukan Masar

17:39 - September 17, 2011
Lambar Labari: 2188698
Bangaren kasa da kasa, an bukaci da a hana mutanen da suke kusa da Husni Mubarak tsayawa takarar neman shugabancin kasar Masar a zabukan da za a gudanar a kasar a cikin lokta masu zuwa.


Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa, jam'iyun siyasa da daman a kasar sun bukaci da a hana mutanen da suke kusa da Husni Mubarak tsayawa takarar neman shugabancin kasar Masar a zabukan da za a gudanar a kasar a cikin lokta masu zuwa a nan gaba.

Wani rahoton kuma ya ce, Firaministan kasar Masar Essam Sharaf ya ce yarjeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin kasarsa ta Masar da gwamnatin mamaya ta yahudawan Sahyuniyya a shekara ta 1979, yerjejeniya ce da ake iya yi wa gyara ko kuma warwarewa a duk lokacin da ka ga dama.

Essam wanda yake zantawa da tashar talabijin mallakar kasar Turikyya a jiya alhamis, ya ce sulhun da aka yi tsakanin Masar da HKI an shi ne dan cin moriyar al'ummomin biyu da kuma dorewar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya amma ba domin amfani wani bangare ba.

Lokacin da aka tambaye shi muhimmanci ziyarar da firaministan kasar Turkiyya ya kai a kasar ta Masar a cikin wannan mako a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Turkiyyar da kuma HKI, a nan sai firaminsitan na Masar ya ce: '' ziyarar ta Tayyip Erdogon tana da matukar muhimmanci musamman ma idan aka yi la'akari da sauye-sauyen da ke faruwa a kasashen Gabas ta tsakiya,

Yana mai cewa dole ne mu mayar da hankali domin tunkarar tushen matsalolin da ke faruwa a yankin wadanda ya ce musabbabinsu shi ne mamaye kasar Palasdinu da yahudawan Sahyuniyya suka yi.

861728


captcha