Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa , ya naklato labar daga shafin sadarwa na yanar gizo na lemonade cewa, sakamakon wani bincike ya tabbatar da cewa irin litatfan da ake yin amfani da su a cikin kasashen nahiyar turai wajen koyar da yara a makarantun piramary da secondary sun tasiri wajen cusa gaba da addinin muslunci a cikin zukatan matasa na wadannan kasashe kamar yaddamuke gani a wannan zamani.
Masana al'amurran yau da kullum sun yi amanna da cewa daya daga cikin dalilan irin wannan makirci da Amurka da sauran kawayenta na kasashen yammaci da wasu na kasashen larabawa suke kulla wa Siriyan shi ne irin goyon bayan da take ba wa kungiyoyin gwagwarmaya a kasashen Labanon da Palastinu da kuma siyasar da ta dauka na fada da bakar siyasar mamaya ta a wannan yankin. A saboda haka ne kasar Amurkan da yahudawan sahyoniyan suke amfani da kasashe irin su Saudiyya wajen tura 'yan ta'adda zuwa kasar Siriyan da nufin aikata aika-aika a can.
A lokacin da yake magana kan wannan lamarin Mr. Stephen Lindman daya daga cikin masana harkokin siyasa dan kasar Amurka ya shaida wa tashar talabijin din kasar Rasha wato Russia Today cewa tun kimanin shekaru biyun da suka gabata kasar Amurka tare da taimakon kasar Saudiyya ta bullo da wani sabon shirin kulla makirci wa kasar Siriyan ta hanyar goyon bayan masu adawa da gwamnatin Siriya da kuma wasu 'yan ta'adda masu dauke da makami na kasashen larabawa wajen haifar da fitina a cikin kasar Siriyan.
Abin da yake a fili shi ne cewa kasashen yammaci da 'yan amshin shatansu na kasashen larabawa sun daura damarar fada da gwamnatin Siriya ta hanyoyi daban-daban musamman ta bangaren kafafen watsa labarai da nufin kawo karshenta, kamar yadda a halin yanzu a ke ganin hakan a fili ta yadda irin wadannan kafafen watsa labarai musamman na larabawa suka matsa kaimi kan Siriya da rufe ido kan irin danyen aikin da masu dauke da makami na kasar suke yi ciki kuwa har da zubar da jinin fararen hula da jami'an tsaron kasar.
861672