IQNA

Akwai Labarai Masu Gamshin Gaskiya Da Ke Cewa Imam Musa Sadre Na nan Da Rai

17:42 - September 21, 2011
Lambar Labari: 2191611
Bangaren kasa da kasa; wasu labarai masu gamshin gaskiya na nuni da cewa Imam Musa Sadre yana nan a raye sai dai labaran bas u yi bayani takamammai kan gurin da ake ci gaba da tsare shi ba amma sun gaskanta cewa yana nan a raye daram .



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wasu labarai masu gamshin gaskiya na nuni da cewa Imam Musa Sadre yana nan a raye sai dai labaran bas u yi bayani takamammai kan gurin da ake ci gaba da tsare shi ba amma sun gaskanta cewa yana nan a raye daram .Kazimi Jalali mai Magana da yawun komitin tsaro da siyasar harkokin waje a mjalisar shawara ta jamhuriyar musulunci tai ran a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya bayyana cewa; haka ne musulmin duniya na cikin damuwa kan makomar Imam Musa Sadre domin kuma yana daya daga cikin wadanda aka fi zalumta da tsare su a gidan yari kuma ya share shekaru masu yawa na rayuwarsa a gidan yari ba tare da iyalansa ko makusantansa ba sun san halin da yake ciki sai dai labarai masu gamshim gaskiya na cewa yana nan a raye.

863975

captcha