Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sayyid Mohmamad Hussaini ministan kula da harkokin al’adun musulunci ya bayyana cewa kur’ani mai tsarki shi ne littafin da ya fi dacewa a kafa dalili da shi wajen hada shirye-shirye na addini da suka hada da fina-finai da kuma sauran abubuwan da za su amfanar da musulmi a kafofin sadarwa na zamanin da muke ciki.
An ambaci wasu daga cikin almun munafukai, wadanda suke fakewa da hujjuji na karya domin su ki zuwa yaki a lokacin ma’aiki, a lokacin da suke baiwa kansu uzuri kuma suna kokarin su raunana zukatan sauran muminai daga zuwa jihadi.
Wannan aya mai albarka ta fallasa irin wadannan mutane, inda take karfafa muminai da su yi jihadi ba tare da karkata zuwa ga rudun abokanin shidan ba, domin gudu daga fagen daga da ake karawa da makiya Allah alama ce ta munafukai masu raunin imani, ayar ta tabbatar mana da cewa muminai na hakika suna yin yaki domin Allah, domin kuwa sun san cewa rayuwar duniya takaitatta ce, abin da ke wurin Allah shi ne dawwame.
Haka nan kuma muminai masu imani na hakika sun suna yin yaki domin aiwattar da umurnin Allah, babu banbanci a wurinsu su yi nasara ko ayi nasara a kansu, yayin da munafukai da suke tare da manzon Allah suna zuwa yaki ne domin riya, sa’annan kuma suna jiran a yi nasara kan kafirai domin su kwashi ganima.
867130