Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wasu mutane dauke da makamai da ba a san ko suwa neb a a daren shekaraen jiya uku ga watan Mehr shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kai wa ofishin liken asiri na Amerika da ke birnin Kabul Fadar mulkin kasar Afganistan hari. Sakamakon masanyar bude wuta tsakanin wadanda suka kai wannan hari da kuma jami'an tsaro masu gadin wannan ofishin liken asiri jami'an tsaron Afganistan uku ne suka mutu akalla. Kuma wannan ba shi ne karon farko a yan kwanaki da watanni da ake kai wa ofishin jakadancin Amerika a Afganistan hari ba lamarin da yake yin nuni da yadda al'ummar kasar ke nuna fushinsu da shiga shigular Amerika da jami'anta a kasarsu.
867328