IQNA

Kiyaye Ka'idoji Na Musulunci Shi Ne Muhimmi A cikin Yunkurin Musulmi

19:01 - September 27, 2011
Lambar Labari: 2194558
Bangaren kasa da kasa, kiyaye kaidoji na addinin muslunci an da matukar muhimmanci a cikin yunkurin da musulmi suke na neman samun 'yanci daga mulkin danniya na shugabanni da sarakuna musamman a cikin kasashen larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, babban mai baiwa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan harkokin siyasa Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa kiyaye kaidoji na addinin muslunci an da matukar muhimmanci a cikin yunkurin da musulmi suke na neman samun 'yanci daga mulkin danniya na shugabanni da sarakuna musamman a cikin kasashen larabawa kamar dai yadda ake gani, a halin yanzu.
Wasu rahotannin sun habarta cewa shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar wajibi ne kasar Iran ta bayyanar da kanta a cibiyoyin kasa da kasa ciki kuwa har da Majalisar Dinkin Duniya don bayyanar da mahangarta kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniya.

Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a daren jiya jim kadan bayan dawowarsa daga tafiyar kwanaki da ya yi zuwa taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen Mauritaniya da Sudan inda yayin da ya ke ishara da ganawar da ya yi da kungiyoyi daban-daban a kasar Amurka Dakta Ahmadinejad cewa ya yi abin da aka sami haduwar baki tsakaninsu shi ne rashin amincewarsu dangane da yadda lamurra suke gudana a Amurkan da kuma cibiyoyin kasa da kasa.

Har ila yau shugaban na Iran ya yi ishara da ziyarar da ya kai kasashen Mauritaniya da Sudan inda ya bayyana alakar da ke tsakanin Iran da wadannan kasashen a matsayin alaka ce mai kyaun gaske, kamar yadda kuma ya bayyana cewar a halin yanzu manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kame ko ina a duniya.

867516

captcha