Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da watsa labaran harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa labarin cewa; Majiyoyin labarai na kasar Turkiya sun bada labarin gano da fahimtar fuskokin sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila da suka kai wa jirgin ruwa na Marmara hari a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta isa yankin gaza na Palasdinu da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta killace.A ranar talatin da daya ga watan mayun shekara ta dubu biyu da goma miladiya ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wa jirgin ruwa ba Maramara da ke dauke day an kungiyoyin fararen hula na kasa da kasa day an jarida hari a kan hanyarsu na kai wa al'ummar yankin zirin gaza agaji bayan da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta killace su inda tara daga cikin yanfaraen hula dad an kasar Amerika daya suka yi shahada lamarin day a jawo Allah wadai da tofin Allah tsine daga kasashen duniya.
868553