Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun kasashen musulmi ta yi kakkausar da yin Allawadai da abin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi na riike kudaden tsohon mai bayar da fatawa na yankin palastinu baki daya bisa zarginsa da hannu wajen karfafa gwiwar masu gwagwarmayar neman 'yanci.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa ba za a taba lamunce wannan cin zalun da haramtacciyar kasar ta yahudawan sahyuniya take yi kan al'ummar yankin palastinu ba, inda ta mayar da su tamkar wasu bayi a cikin yankunansu, inda kungiyar ta yi kira ga manyan kasashen duniya da su safke nauyin da ya rataya kansu.
Rahoton ya ce kungiyar bunkasa ilimi ta kasashen musulmi ta yi kakkausar da yin Allawadai ne da abin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi na riike kudaden tsohon mai bayar da fatawa na yankin palastinu baki daya, saboda hakan ya sabawa dukaknin dokoki na kasa da kasa.
870058